Type Here to Get Search Results !

CIKAKKEN BAYANI AKAN ASUSUN PAYPAL

MENEN MAANAR ASUSUN PAYPAL A turance shine PAYMENT SYSTEM 

PayPal wani asusu ne da zai baka damar biyan kudi, tura kudi, dakuma karbar biyan kudi. Zakayi rijistar asusun ka na PayPal  ne da katin ATM dinka na banki wato credit card ko kuma debit card. TAYAYA AKE AMFANI DA ASUSUN PAYPAL

A yayin da kaje yin siyaya a Internet ta kaya ko wani abu zaka iya zabar asusun PayPal don biyan wannan kudin kaya. 

Haka zalika sautari wasu camfanoni a Internet basa yarda da kowanne asusu idan bana PayPal ba kamar su eBay da sauransu. 

Wannan dalili ne yasa duk lokacin da kayi siyayya a Intanet to dazarar kazoo wurin biya sai kadau PayPal. 


ABIN LURA:
Shi asusun PayPal zaka iya siyan kayan miliyoyin naira dashi ba tare da wata matsala ba, kuma yafi sirri kasancewar duk lokacin da zakayi wani ciniki a Intanet saika tura iya adadin kudin da zakayi siyayyar dasu a asusunka na PayPal sai kayi siyayarka dasu.  Kaga kenan babu wani da zaisan sirrin asusunka na banki. 

MEYE DAMARKA A MATSAYINKA NA PAYPAL MEMBA:

Zaka iya tura kudi daga asusun bankinka zuwa asusunka na PayPal. 

Tura kudi daga asusunka na PayPal zuwa wani asusun PayPal.

Tura kudi daga asusunka na PayPal zuwa asusunka na banki. 

Zaka dinga samun sakon email na duk wani aikace-aikace na asusunka na PayPal. 

Zaka iya samun kati na PayPal (debit card) don yin siyayarka a fadin duniya 

Zaka iya sanya katinka na banki sama da daya a asusunka na PayPal. 

        Kayi kokarin turawa a WhatsApp Mungode kana iya tambayar abin da yashigema duhu.