Type Here to Get Search Results !

Kadda Kayi Gaugawar Yanke Hukunci Idan Kaji Wannan LabarinWata rana wani likita yayi saurin tafiya asbity yayin da yasamu kira daga asbityn da yake aiki donyiwa wani karamin yaro tiyata. 


Likitan ya canza kayan dake jikinsa ya tafi asbityn da sauri. Shigrsa ke da wuya ya tafi bangaren yan tiyata. Uban yaron kuwa yana ta faman duba agogo, kwatsam saika likita 

Zuwan likitan keda wuya sai uban yaron nan ya fara fada yana cewa meye ka tsayayi harkakai wannan lokacin bakazoba, shin bakasancewa rayuwar dana tana cikin hadariba ko dan ba yaronka ne ke cikin halin yin tiyata ba. 

Likitan ya saukakar da muryar sa yace kayi hakuri nazo ne a iya bakin kokarin sauri na, ka kwantar da hankalinka yaronk zai warke. 

Uban yaron ya kuma cewa cikin fada, idan da Yaronka ne cikin dakin tiyatar da tuni kai masa abinda ya dace ai, likita yace kayi hakuri zanyi iya bakin kokari na don danka ya samu lafiya, uban yaron yace wannan kadai zaka iya fada. 


Likita ya shiga dakin da yaron yake ya fara aikin cikin nutsuwa, aikin ya dauki lokaci mai tsawo kafin likitan ya kammala. 

Likita yasamu nasarar kamala aikinsa, yafito yasamu uban yaro yace masa yaronka zai samu lafiya, ni na wuce. 

Kafin uban yaron  yace wani abu tuni likita ya fice daga  asbityn  da sauri. 

Uban yaron yace aa meye matsalar wannan likitan bai banni nayi masa tambaya akan dana ba yayi tafiyarsa abinsa. 

Likitar da uban yaron ya fara samu a cikin asbityn wadda itace ta kirawo masa likitan tiyatar kawai sai ta fashe da kuka tacewa uban yaron ai jiya dansa ya mutu yayin hadarin mota, likitan yana wurin binne dan nasa ne muka kirashi shine ya bar binne dan nasa ya taho don ceton naka yaron. 


Yanzu ya gama tiyatar yaronka don haka ya wuce don gama sallatar yaronsa. 
Darasin wannan Labari:


kayi tunani kafin yankewa mutane hukunci. Domin bakasan ya rayuwarsu take ciki a wannan lokacin yanke hakuncin naka ba. 


Katura wannan labari zuwaga yan uwa
Rubutawa - Rabswudil

Tags