Type Here to Get Search Results !

Labari Mai Muhimmanci Ki Daure Ki Karanta Don Afanin Kanki.






LABARIN WATA MATA MAI AIKIN NAMA

Takansance tana  aiki a wata masana'antar saida nama ga masu bukata. 

Wata rana bayan tazo wurin aikinta ta kuma kamala aikin, Sai ta tafi dakin sanyi wato inda ake ajiya naman da ba'a sayarba (meats Cold freezer) don yin bincike akai. 



Shigar dakin nata ke da wuya sai kofar dakin sanyin ta rufe Ruf. 



Tayi - tayi ya bude amma ina kofa taQi budewa tayi bugu iya bugun kofar ko Allah zaisa wani yajita ya kawo mata dauki amma ina babu wada yaji. 



Tayi kuka iya kuka amma ina babu wanda yajita, kuma sanyin dakin yafi karfin dan adam ya iya jure shi zuwa wani lokaci. 



Gabadaya ma aikatan masana'antar suntafi maana sun tashi a aiki. 



Bayan kamar awanni 5 Tana daf da mutuwa a cikin dakin sanyi , katsam sai mai gadin masana'antar ya bude kofar. 



Bayan ta dawo daga hankalinta, sai take tambayar  mai gadin Tayaya har kazo ka bude wannan kofar bayan baka saba hakaba? 



Sai mai gadin yace, nayi aiki a wannan ma aikatar na tsawon shekaru 35, kullum ma aikata sama da 100 suna shige da ficewa a kullum, 



Amma kadan daga ire-iren ku idan sunzo aiki suke gaisar dani haka idan zasu fita sai sunce min suntafi maana sai munyi sallama dasu cewa suntafi, kuma hakan ina matukar jin dadinsa, saboda wasu suna daukata kamar bakomai ne niba a wannan lokaci kasancewar ni mai gadi ne. 



Yauma kamar kulluma lokacin da kikazo aiki mun gaisa dake kamar yadda kika saba. 



Amma bayan an tashi daga aiki inata zuba ido inga cewa kinzo munyi sallama amma sai naga kwata-kwata ban ganki ba. 



Don haka sai naita tunanin meye yafaru dake haka BABBAN ABIN DA NAKE TUNAWA SHINE IRIN YADDA KIKE KOKARIN GAISAWA DANI A KULLUM, saboda kina nunamin ni mutum ne don haka dabanji hakan ba nasan cewa akwai wani abu da yafaru dake a gidan nan. 

Hakan tasani na bazama inta bincike a cikin wannan masana'antar lungu da sako ko ina ban ganki ba har nayi kokarin fita sai nace bari in duba dakin sanyi wato (meants Cold RooM) in budewa na ganki. 



DARASI::



Kuzama mai Hakuri biyaya da nuna kawaici fara'a da kulawa ga duk matanan da suke kusa daku,  Domin kuwa hakan zaisa duk abinda ya faru daku a dinga yawan tunawa daku kamar dai yadda ya faru da wannan baiwar Allar. 

Allah yasa mudace Amin.
Tags