Type Here to Get Search Results !

Karanta Wannan Labari Kaji Ikon Ubangiji







Wata rana da yamma wasu ma'aurata na tafiya cikin wata mota a wani babban titi. 

Sunyi tafiya mai nisa katsam sai suka hangi wata mace a gefen titin tana sanya musu hannu alamun su tsaya, Matar tacewa mijin mai gida kada katsaya domin bamusani ba ko ta shirya mana wani makircine. 

Mai gidan baiyi magana ba kawai sai ya taka birki ya koma baya, fitiwarsu keda wuya sai suka fahimci matar duk taji raunuka a jikinta ga jini ko ina a jikinta. 

Suka tambayeta lafiya sai tace sun samu hadari ne da mota amma mijin ya mutu sannan akwai yaronsu a cikin motar amma shi da ransa. 

Nan da nan mutumin da ya tsaya don taimako ya fada cikin wannan rami shigarsa keda wuya sai yaga mutane biyu mace da namiji a gaban mota sai yaga basu ya kmata ya fara ceta ba tunda akwai yaro. 

Kai tsaye ya tafi kujerar baya saiga yaro yana ta kuka ya sanya hannu ya dauki yaron y fito dashi, fitarsa keda wuya sai yaga baiga matar data tsaidasu don neman taimakonsu ba, saiya tambayi matarsa ina wannan matar kuma sai tace ai yayin daka shiga cikin ramin matar ta bika, nan da nan ya mika yaron hannun matarsa ya koma ramin. 



Shigarsa keda wuya sai yaga cewa matar data tsaidasu don neman taimako itace a gaban motar ga kuma bell ta daure jiki a jikinta ita da mijinta. 

Ya kura ido yaga cewa lallai itace a gaban motar. 

Sai yace lallai Allah Buwayi gagara misali ne. 

Darasin Da Muka Koya:
1. Idan kana cikin Wani kunci kayi kokarin sanya Allah a zuciyarka, Zaka samu sauki daga gareshi.
Tags