Type Here to Get Search Results !

Dalilan Mace Macen Aure A Zamanin Nan

 


Daga cikin babban aikin SHAIDANU shine raba tsakanin mutane da haddasa husuma a tsakaninsu musamman ma ma'aurata.

Shi yasa Shaidanu suna daga cikin dalilan yawancin mace-macen auren da ake samu ga yawancin sababbin ma'aurata a wannan zamanin, ko dai ta hanyar Sihiri ko Kambun-baka ko hassada ko kuma shafar jinnu.

Za ka samu yarinya kafin aurenta tana dauke da jinnu a jikinta amma basu taba bayyana ba sai dai wasu alamu amma ita ko iyayenta ba sa kawo komai akai sbd ai basuga suna bayyana ba, hakan sai yasa su share batun suki daukar wani mataki, nan kuwa abin ya gawurta sunyi fakare ne da likimo.

Sai kaga bayan aurenta ne abubuwa da alamun su suyita bayyana kala-kala, har su rika sabbaba manya-manyan rikice-rikice wadanda za su iya kaiwa ga rabuwar auren gaba daya. daga cikin alamomin akwai:

1- Tarika Jin haushin mijinta haka kurum ba tare da ya yi mata laifin koma ba.

2- Ko idan tana zaune a cikin gidan sai ta rika jin kunci da damuwa, amma idan ta fita sai taji duk babu wannan damuwar.

3- Kafin mijin ya shigo tayita walwala tana fara'a, amma Idan mijin ya shigo sai taji komai ya sauya tayita faman shiga kunci da damuwa.

4- Ta rika jin bazata iya zama a gidan ba sbd ya isheta.

5- Tayita neman saki akai akai haka kurum ba tare da wani dalili ba.

6- Rashin yin uzuri akan wani dna karamin kuskuren da bai kai ya kawo ba.

7- Ko dai Aljanun su rika bayyana maa akai-akai, alhali kuwa a baya can kafin tayi aure ba ta yi.

ALLAHu A'alam.

Ku zamto masu boye neman aurenku, idan aka kawo miki lefe ko anyi miki baiko ki rika boyewa ba wai kiyita yayatawa a Social Media kowa yana gani ba, irin haka Kambun-baka da hassada za su iya shiga ciki suyi tasiri a cikin zama aurenki amma ba zasu iya tabbatar da komai ba sai da IZININ ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

MARUBUCI: Abu Nu'aym
Tags