Type Here to Get Search Results !

Yadda Zaka Mallaki Zuciyar Matar Ka.

 Na sha tattaunawa da wasu mata daga cikin ƴan-uwana da iyaye, sai na fahimci mace tana matuƙar son yabo da jinjina, saboda haka duk lokacin da mijinta yake yabon ta, to ta kan shiga wani farin ciki wanda ba ya misaltuwa. 


Ta ɓangare ɗaya kuma mace ta kan rayu cikin takaici idan aka jarabce ta da miji wanda ba ya iya yabo da jinjina ba. Za ka ji tana cewa: 'ko na yi kwalliya aikin banza ne', 'sai mutum ya ɓata lokaci ya girka abinci amma ba za'a yaba ba, da sauran zantukan da suke nuna takaici a kan haka.


Yabo tukuici ne mai girma ga mace a duk lokacin da ta yi bajinta, kai wani lokacin ma mace ta kan fifita yabo a kan kyautar kuɗi (ba tare da yabo ba).


Idan kana so ka mallaki zuciyar matarka to ka riƙa yabon ta a cikin abubuwa guda takwas:


1. Surar/jikinta; Misali: Gaskiya wance ke kyakkyawa ce, tsayinki yana burge ni, idanunki suna ɗaukan hankali, gashi har gadon baya, d.s.s


 2. Zancenta; Misali: Sarauniyata zancenki yana saka ni cikin natsuwa, uwargida akwai hikimar zance, da kowace mace zata iya magana irin taki da gidaje sun zauna lafiya, d.s.s


 3. Tufafinta; Misali: Siwithat wannan wanka kamar ba za'a mutu ba, tufafinki sun burge ni, wannan wanka ya cancanci tukuici, kayan nan sun dace da ke, d.s.s


 4. Abincinta; Misali: Wannan abinci ya yi daɗi sosai, wannan miya ta yi zaƙi sai kace zuma, d.s.s


 5. Yaron/yaranta; Misali: Aliyu akwai tsafta, ƙoƙari, natsuwa; ba mamaki mahaifiyarsa ya biyo, kina ƙoƙari game da makamantar yaran nan, d.s.s


 6. Gidanta; Misali: Habibiya kullum gidanki yana cikin tsafta, idan ina cikin daƙinki ba na son fita saboda ƙamshi, d.s.s


 7. Addininta; Misali: Gimbiya riƙo da addininki yana ƙayatar da ni, na yi babban dace da samu mai addini irinki, ba na gajiya da sauraren karatun Alkur'aninki, d.s.s


 8. Hankalinta; Misali: Malam na yaba da hankalinki, ina godiya ga Allah da ya azurta ni da mai hankali irinki, d.s.s


Ya kamata miji ya san yaren mace a lokacin da ake yabon ta. Duk lokacin da kake yabon matarka idan ka ji ta ce ka dena to abin da take nufi shi ne ka cigaba. Wani lokaci zaka yabi mace amma sai ta nuna kamar ba ta gamsu/yarda da yabon da kake yi ma ta ba, yadda al'amarin yake tana faɗa maka ne ta gamsu.


Idan baka saba yabon matarka ba to ka koya. Kar ka manta duk lokacin da kake yabon matarka lada kake samu, saboda kalma mai daɗi sadaka ce.


Daga Zauren.

MAJLISIN AL-QALAMUL MUSTAAMAL

Tags