Type Here to Get Search Results !

[FACEBOOK] KAYI KOKARIN GOGE WADANN ABUBWA DANA LISSAFO A KASA

RabiuBlog




Ya kamata mutane su daina yadda da abinda  kafafen sadarwa ke shiryawa don rubuta muhimman bayanan su. Sauda dama kafafen sadarwa irinsu Facebook da Twitter da Makamantan  irinsu kan bukaci mutum ya sanya duk wani muhimmin bayaninsa a yayin da yake register. 


Wanda hakan yakansa wasu su saki jiki su sanya dukkanin bayanan su a wurin, wanda akarshe hakan kanzama illa ga wasu, wasu kuma ba su san illar yin hakan ba. 


Yakai dan uwa mai karatu kasani cewa sakin jikink ga kafafen sadarwa wajen rubuta duk wasu muhimman bayanan ka ba karmar matsala bace wanda hakan ne ma yasanaya muka tsakulo muku muhimman abubuwa guda shadaya da da bai kamata kasanya su a kafafen sadarwa ba. 


Ina mai baka shawara da zarar ka kammala wannan karatu to Kayi saurin gogewa don gudun bacin rana allah ya kiyayemu da ita. 



Zamu dau kafar sadarwa ta  Facebook da Twitter 



1. GOGE MUTANAN DA BAKU SANIBA
Sau dayawa mutum kan sanya mutanen da bai sansu ba a Facebook ko twitter kawai don idan sunyi posting suyi musu like ko comment, dan uwa kasanya mutanan da kasani ko kayarda dasu kawai. 



2. RANAR HAIHUWAR KA. 
Sanya ranar haihuwar ka a Facebook ko twitter kansa mutane su samu damar satar bayanan ka na sirri cikin sauki. Dan uwa da mutane sudinga yimaka muranar ranar haihuwar ka gara karsuyi don tsira daga miyagun mutane. 




3. SANYA HOTUNAN YARANKA/KI. 
Sanya hotunan yaranku a Facebook ko twitter kan bawa masu karkuwa da yara damar satar yayayenku cikin sauki.  Don haka kuyi kokarin goge hotunan yaranku in har kunsanya su. 



4. LAMBAR WAYARKU
Sanya lambar waya a Facebook shima wata gagarumar damuwa ce, domin kuwa duk wani adreshin ka zaa iya samun sa ta bibiyar lambar wayarka, kamar wani rahoto da NSPCC ta bayar cewa mafiya yawan zinace-zinace yana faruwa ne ta hanyar sanya lambobin waya a shafukan Internet a Ingila da Amuruka. 



5. GURIN DA KAKE (LOCATION) 
Yawancin mutane kan bayyan inda suke a kafafen sadarwa wanda hakan kanjanyo masu garkuwa ko barayi suyiwa mutum illa. 



6. BAYANAN BAKIN KU
Idan ya kasance kana samun kudi a Facebook ko kuma sanya talla a shafin Facebook Kayi kokarin goge duk wani bayanai naka na debit card don gujewa satar kudinka ga yan kutse. 



7. TIKITIN TAFIYE-TAFIYE
Kada kusake kusanya tikitinku na tafiya zuwa wata kasa. 



8. SANYA WANI OGANKU A MATSAYIN ABOKIN FACEBOOK 
Kada kusanya oganinku a Facebook har saidai  idan sun daukeku a matsayin abokan juna. 



9. BAYANAN SIRI
Sanya bayanan sirri a shafu nan ku na Facebook kamar. "Gashi natafi wani wuri" ko kuma "gashi ina cikin wani wuri" dadai sauransu.. Shima kudos na sanya wa. 




10. ADDRESHI
Sanya addreshin ku a kafafen sadarwa kansaya miyagun mutane su samu damar sanin inda kake cikin sauqi. 

Duk wadan nan abubuwa da muka lissafa ya kamata mai karatu ya kiyaye su idan kuma ka riga kasanya wani to Kayi kokarin share shi Allah ya kiyaye. 

Tags